Labarai
Hukumar INEC ta musanta rade-radin cewa ba za ta yi amfani da na’urar Card Reader ba a zaben gwamnoni da ‘yan majalisu
Hukumar zabe ta kasa INEC ta musanta rade-radin cewa ba za ta yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a ba watau Card Reader a yayin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi wanda za a yi a ranar Asabar 9 ga wannan wata da muke ciki na Maris.
Kwamishina mai kula da wayar da kan jama’a na hukumar Festus Okoye ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce tun bayan zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokokin tarayya da aka yi a ranar 23 ga watan jiya na Fabrairu, wasu ‘yan Najeriya ke zargin cewa hukumar ta nuna son kai wajen amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a watau Card Reader.
A cewar Fetus Okoye zargin ne ya janyo wasu ke ta yada rade-radin cewa me yiwuwa hukumar ta gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi ba tare da amfani da na’urar Card Reader ba.
Kwamishinan wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar ta INEC ya kuma ce babu kanshin gaskiya cikin zargin da kuma rade-radin; yana mai cewa hukumar za ta yi amfani da na’urar Card Reader a zabukan na ranar Asabar me zuwa.