Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutane 40 sun mutu a sabon harin da ‘Yan binding suka kai a Zamfara.

Published

on

Ana zargin mutane 40 ne suka rasa rayukan su a wani sabon harin da ‘Yan binding  suka kai a kauyuka 2 da ke jihar Zamfara.

Awanni 24 ne kenan bayan da gwamnan jihar ta Zamfara Abdulaziz Yari  ya yi alkawarin cewa zai kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso tsakiya na jihar.

Abdul’aziz Yari, ya kara da cewa Gwamnatin sa ta baiwa hukumomin tsaro umarnin da su bankado ‘yan bindigar don fuskantar hukunci mai tsanani.

Sabon harin dai ya afku ne a yankin Danjibga da sauran yankuna cikin karamar kananan hukumomin Shinkafi da Anka, yayin da ‘yan bindigar suka yi amfani da Babura wajen kai hare-haren.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ta Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da afkuwar alamarin yana mai cewa bayan mutum 40 da suka rasa rayukan su, kawo yanzu rundunar na cigaba da bincike kan irin asarar da aka tafka.

SP Muhammad Shehu ya kuma sheda cewar nan gaba kadan ne rundunar zata yi taron manema labarai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!