Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta tsayar da 13 ga wannan wata da muke ciki don gudanar da zaben cike gurbi na sanatan Anambra ta tsakiya
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta tsayar da ranar 13 ga watan Janairun da muke ciki a matsayin ranar da zata gudanar da zaben cike gurbi na sanatan Anamra ta tsakiya.
Kwamishinan zaben jihar ta Anambra Dr Nwachuku Orji ne ya bayyana haka ga manema labarai da yammacin jiya inda ya ce matsalolin da suka hana gudanar da zaben a baya an magance su.
Ya kuma ce bangaren shari’a yayi nazarin na hukumar yayi nazari kan hukuncin da kotu ta yanke ya kuma umarci hukumar da ta gudanar da zaben kamar yadda kotun daukaka kara ta bada umarni, wanda ya saba da hukuncin da wata kotun tarayya tayi a baya na dakatar da zaben.
Dr Oji ya ce tuni hukumar da fara baiwa Jami ‘anta da za su gudanar da aikin zaben horo na musamman kan yadda zasu gudanar da zaben.
Ita dai mazabar Danmajalisar Dattawa ta Anambra ta tsakiya ta kasance bata da wakili majalisar dattijai tun a shekarar 2015, tun da kotun daukaka kara ta kori wanda ke kan kujerar Misi Uche Ekunife.
Haka kuma kotu ta baiwa hukumar zaben umarnin gudanar da zaben cike gurbin a tsakanin kwanaki 90 da hukuncin kotun inda kuma ta haramtawa wadda ta saukar sake shiga zaben da ma jam’iiyar ta ta PDP.