Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun fitar da jadawalin karshe na zaben cike gurbi – INEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC ta fitar da jadawalin karshe na yadda zaben cike gurbi na gwamnan jihar Ondo zai kasance a ranar 10 ga watan Octoban shekarar da muke ciki.

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kai na hukumar zabe ta kasa INEC Festus Okoye ya fitar a Abuja.

Okoye ta cikin sanarwar ya bayyana cewa jadawalin wanda hukumar ta INEC ta aike da shi zuwa kananan hukumomin da ke jihar ta Ondo kuma za a iya samun jadawalin a Website din hukumar.

Sanarwar ta bayyan cewa hukumar ta sanya ranar 18 ga watan Agusta ya zamo ranar da za a kammala karbar takardun sunayen yan takara a kowacce jiha sai dai har kawo yanzu jam’iyyu hudu ne kacal suka mika da takardar sunayen ‘yan takarar ta su.

Ta cikin sanarwar dai, Okoye ya ce hukumar a zamanta na ranar alhamis ta yanke hukuncin fara gabatar da zaben gwamnan jihar Ondo da kuma sauran zabubbukan cike gurbi da za gudanar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!