Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB ta bukaci dalibai da su fara fitar sakamakon jarabawarsu

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da Sakandare ta kasa JAMB; ta bukaci dalibai da su fara fitar da takardar shaidar jarabawarsu wato examination notification slip daga shafin website na hukumar daga gobe Talata.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar Dr. Fabian Benjamin ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Lagos.

Ya ce tuni komai ya gama kankama domin rubuta jarabawar wanda za a fara ranar juma’a tara ga watan da muke ciki a kuma kammala a ranar sha bakwai ga wata.

A cewar sa nasarorin da hukumar ta samu wajen jarabawar gwaji da ta shirya a ranar 26 ga watan jiya na Fabrairu shi ke nuna cewa jarabawar na bana akwai alamun nasara.

Mai magana da yawun hukumar ta JAMB ya kuma ce wajibi ne ga duk dalibin da zai rubuta  jarabawar da ya tabbatar da cewa ya cire takardar jarabawar daga website din hukumar kafin nan zuwa ranar juma’a tara ga wata wanda za a fara rubuta jarabawar, duk kuwa dalibin da ya gaza haka to ya tabbatar da cewa ba zai rubuta jarabawar a bana ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,926 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!