Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

JAMB ta fitar da katin jarabawar gwaji kafin UTME

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB ta ce katin jarrabawar gwaji ta tantancewa ta UTME da za a gudanar ya fito, kuma dalibai za su iya shiga shafinta na intanet domin fitarwa.

Wannan na cikin sanarwar da ofishin shugaban hukumar ya saba fitarwa mako-mako a Abuja.

Akwai cikakkun bayanai na ko wane dalibi a cikin takardar da za a fitar ta shafin, da suka hadar da suna da lamba da kuma wurin da za a rubuta jarrabawar.

Hukumar ta kara da cewa jarabawar gwajin ba dole bace amma tana da muhimmanci ga duk dalibin da yake bukatar gwada kwazon shi kafin zuwan jarabawar UTME.

Za dai a gudanar da jarabawar gwajin ne a ranar Alhamis 20 ga wannan watan na Mayu da muke.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!