Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB ta ce ta shirya tsaf don fito da bayyanan yadda ta kashe kudadenta

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB ta ce ta shirya tsaf don fara fitar da kundin bayanan yadda ta ke kashe kudaden ta, don kauda shakku a zukatan al’umma da kuma fito da komai fili.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar Dr. Febian Benjamin ne ya bayyana hakan a yayin da yake tattaunawa da manema labarai a yau litinin a jihar Lagos.

Benjamin yace za’a rika wallafa kundin, wanda aka yiwa suna da Jambulletin duk ranar litinin, inda yace ba sayarwa za’a rika yi ba.

Ya kuma kara da cewa hukumar zata fara sayar da fam na rubuta jarabawar ta JAMB ta shekarar 2019 a ranar 10 ga watan janairun da muke ciki.

Sannan ya kuma ce ba wai iya batutuwan kudi kadai kundin zai kunsa ba, har ma da bayanan nasarorin da hukumar ta ke samu da kuma yadda ta ke gudanar da ayyukan ta don amfanin al’umma.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,480 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!