Connect with us

Kiwon Lafiya

Tashin hankalin da aka shiga a Libya na daga cikin dalilan samun tashin hankali a Najeriya-shugaba Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, tashin hankalin da aka shiga a kasar Libya na daya daga cikin dalilan da suka sa ake samun tashin hankali a Najeriya.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da gidan rediyon Muryar amurka inda ya ce hakan ce ta tilastawa makiyaya dake yawo da sanda suka fara daukar bindiga.

Shugaba Buhari ya ce duk da cewa al’umma na alakanta  rikicin Fulani da Makiyaya da kabilanici da kuma addini, amma a zahirin gaskiya wahalar da ake samu na da alaka da shigowar mutane daga kasashen ketare musamman ma kasar libiya

Shugaban kasar ya kuma ce barnar da aka yiwa tsarin da magabatan shugabannin  irinsu Sardauna suka yi wadanda suka samar da burtaliai ga makiyaya, aka yi dam-dam aka kuma sa famfo mai amfani da iska, wadanda masu hali suka dauka suka maida manyan gonakin su , ya zama sanadin matsalar da ake ciki yanzu.

Ya kara da cewa, mutanen da ake kashewa a Zamfara sun fi wadanda ake kashewa a Taraba da Benuwe yawa, amma sai a rika cewa, sha’ainin addini ko kabilanci ne yak e faruwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,589 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!