Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB ta tsayar da 6 ga watan gobe a matsayin ranar rufe sayar da form din jarrabawar shekarar nan

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu JAMB, ta tsayar da ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar nan a matsayin ranar da zata rufe sayar da form din zana jarrabawar ta shekarar bana.

Shugaban hukumar ta Jamb Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka yayin taron tsare-tsare da kuma sanya ido yayin gudanar da jarrabawar ta jamb na bana da ya gudana jiya a Abuja.

Ya kuma ce kawo yanzu mutane dubu dari biyu da tamanin da uku da dari uku da sha tara ne suka yi rijitar zana jarrabawar.

Hukumar ta kuma tsayar da ranar 9 zuwa 17 ga watan mayu a matsayin ranar da za a gudanar da jarrabawar inda aka shirya gudanar wa a cibiyoyin kwamfuta 620 a fadin kasar nan.

Farfesa Oloyede ya ce hukumar ta sauya ranar 22 ga janairun da muke ciki domin shirya jarrabawar gawji wato Mock zuwa farkon satin watan fabrairu mai kamawa.

Haka kuma hukumar ta ce ta haramta shiga da agogo da biro da fensiri da dukkanin kayan amfani da ga shiga da su dajin jarrabawar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!