Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Kano zata samar da Sabuwar shelkwatar hukumar Hisbah ta bayar da horo na musaman

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta samar da Sabuwar shelkwata mai girma ga hukumar Hisbah wadda za’a yi amfani da ita wajen bayar da horo na musaman ga jam’an na Hisbah.

Gwamana Kano Abdullah Umar Ganduje ne ya bayyaan haka yayin da yake karbar bakuncin malaman da suka dawo daga taron bitar karawa juna sani kan harkokin addinin Musulunci daga kasar Masar.

Gwamna Ganduje ya ce an tura malaman ne domin karo sanin Makamar aiki duba da yadda wasu bara-gurbi ke sanya wa ana yiwa addinin Musulunci kollon addinin ta’addanci.

A nasa jawabin mai baiwa Gwamnan shawara kan harkokin addinai Ali Baba Fagge, ya ce shirin wanda hadin gwiwa ne da hukumomin Saudiyya zai karbi kashin farko da za su ta shi zuwa madina domin karbar horon.

Daya daga cikin wadanda suka dawo daga masar dan sheikh Yusuf Paki ya ce sun amfana da abubuwan da dama a can.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!