Labarai
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano ta tantance tare da yi wa maniyyata 1,253 riga-kafi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Kano, ta tantance lafiya tare da yi wa maniyyata kimanin 1,253 riga-kafi domin shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’inta na hulɗa da jama’a na Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar.
Ta cikin sanarwar, Sulaiman Dederi ya ce, an gudanar da gwajin lafiya da riga-kafin ne a asibitin sansanin Alhazai, inda aka tattaro maniyyta aikin Hajji bana daga ƙananan hukumomi 20.
A cewarsa, an yi wannan shiri ne domin tabbatar da cewa duk maniyyatan su na cikin ƙoshin lafiya kuma sun karɓi riga-kafin da ake buƙata bisa ƙa’idojin lafiya.
Hukumar ta cijkin sanarwar ta kuma jaddada aniyarta ta ganin an gudanar da aikin Hajjin cikin sauƙi da tsari, tare da ba da fifiko ga lafiya da tsaro, ta kuma ce za a ci gaba da tantancewa da yi wa sauran maniyyata riga-kafi kamar yadda aka tsara.
You must be logged in to post a comment Login