Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NAHCON za ta fara yi wa maniyyata binciken lafiya

Published

on

Hukumar jin daɗin alhazai ta birnin Tarayyar Abuja, ta bayyana ranakun 5 zuwa 7  ga watan Mayu a matsayin ranar da za ta fara gudanar da bincike lafiya ga maniyyatan bana.

Daraktan hukumar Malam Abubakar Evuti, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar Malam Muhammad Aliyu ya fitar a Talatar nan.

Shugaban ya ce, za a fara yi wa maniyyata aikin hajjin bana allurar riga-kafin daga 15 ga watan na Mayu zuwa 17 ga watan, saboda a samu kammala shirye-shiryen maniyyatan da wuri.

Haka kuma, ya shawarci maniyyata da su tabbatar sun yi duk abubuwan da hukumar ta gindaya domin ba su damar gudanar da aikin hajjin yadda ya kamata.

 Malam Abubakar Evuti, ya ja kunnen waɗanda har yanzu ba su mayar da fom dinsu ba da su hanzarta yin hakan ta hanyar kai fasfo ɗinsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!