Labarai
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano na ci gaba da shirye-shiryen aikin bana
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta bukaci alummar kasar nan da su kwantar da hankali su bisa ga umarin da hukumomin kasar saudiyya suka bayar na dakatar da dukanin shirye-shiryen aikin hajin bana sakomakon cutar covid 19 ake fama da ita a duniya.
Shugaban hukumar Abdullahi Saleh Fakistan ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi nan freedom radiyo, wanda ya mayar da hankali kan umarnin dakatar da shirye-shiryen aikin hajjin bana da kasar Saudiyya ta bayar.
Ya ce har yanzu hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen ta, kasancewar wannan umarni har yanzu bai je wa hukumar, a hukumance ba.
A nasa bangaren, shugaban kamfanin shirya tafiye-tafiye na Hamsun, Alhaji Mustafah Hamisu ya ce akwai bukatar wadanda suka riga suka biya kudaden Umara su kara hakuri, kasancewar kamfanoni irin nasu na kokarin mayar musu da kudaden su, tunda babu maganar tafiya a halin yanzu.
Bakin sun kuma shawarci al’ummar musulmai da su kasance masu bin dokokin masana harkokin kiwon lafiya da gwamnati, tare da gyara tsakanin su da mahaliccin su, don ganin an shawo kan wannan annoba da ta addabi duniya.
You must be logged in to post a comment Login