Labarai
Hukumar jin dadin Alhazai ta Kano ta fara raba kayayyaki ga maniyyata

Hukumar Jin Dadin alhazai ta Jihar Kano ta fara rabon kayayyakin aikin Hajjin bana ga maniyyata da za su tafi kasa mai tsarki.
Shugaban hukumar Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar.
Sanarwar, ta bukaci dukkan masu manniyatan bana da su yi amfani da kayan da aka raba musu yadda ya kamata, tare da kauce wa daukar wasu kayan da hukumar kasar Saudiyya ta haramta.
Haka kuma ta umurci maniyyatan da su tuntubi jami’an aikin Hajji na kananan hukumominsu domin karbar kayayyakin.
Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ta cikin sanarwa ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, da ta sake duba batun amfani da katin ATM wajen bayar da kudin guzuri ga maniyyata.
You must be logged in to post a comment Login