Labarai
Hukumar jin dadin Alhazai ta Kano ta fara yi wa maniyyata allurar riga-kafi

Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano, ta fara yi wa maniyyata aikin hajjin bana allurar rigakafi da kuma duba lafiyar su.
Shugaban hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbaffa, ne ya kaddamar da fara aikin riga-kafi da duba lafiyar maniyyatan.
Da ya ke jawabi yayin kaddamarwar, Alhaji Lamin Danbaffa, ya kara da cewa hakan na daga cikin manyan shirye-shiryen da suka kamata hukumar ta yi domin kauce wa samun matsalar rashin lafiya lokacin tafiya ibadar
Da take jawabi, jami’ar kula da lafiya ta hukumar jin dadin Alhazai ta Kano Hajiya Hindatu Mukhtar ta ce, an tanadi dukkan kayayyakin aikin da suka dace domin tabbatar da cewa kowanne maniyyaci ya samu allurar rigakafinsa a lokacin da ya dace.
You must be logged in to post a comment Login