Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA ta cafke mota cike da Barasa

Published

on

 

 

Hukumar kula da zirga zirgar ababan hawa KAROTA ta cafke wata mota kirar Bus dake dauke da barasa da miyagun kwayoyi.

An cafke motar ne akan titin Sanwa Olu daKe unuguwar Sabongari lokacin da dakarun hukumar ta KAROTA ke bincikar ababan hawa dake dauke da lodin kayayyaki.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jamaa na hukumar ta KAROTA Nabulusi Abubakar Kofar Naisa ya sakawa hannu tace jamian hukumar ta KAROTA sun bi motar inda suka kame Kwandastan motar mai suna Bila inda kuma direban ya tsere.

Nabulusi Kofar Naisa ya kara da cewa an mika barasar ga hukumar Hisba domin cigaba da bincike.

Sanarwar ta Hukumar KAROTA ta bukaci da a cigaba da bayar da rahotanni akan duk wani abu da kai ya jawo karya doka ga hukumar ta KAROTA da sauran hukumomi a na tsaro jihar Kano.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!