Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ilimin ‘ya’ya mata zai gyara rayuwar al’umma –Yariman Kano

Published

on

Yariman Kano Alhaji Lamido Abubakar Bayero yace matukar mata suka yi amfani da Ilimin Addinin musuluncin da suke nema musamman wajen koyarda ‘ya’yansu shakka babu alamune dake nuni da cewa za’a samu ingantacciyar Al’umma, kasancewar iyaye mata sune ke tare da ‘ya’ya dare da rana.

Alhaji Lamido Abubakar Bayero ya bayyana hakan ne lokacin taron saukar karatun Alkur’ani mai girma na makarantar Madrasatul Anwar Al-Islamiyya Litahfizul Qur’an dake unguwar Sabuwar Gandu a karamar Hukumar Kumbotso.

Yariman Kano Lamido Bayero ya kara da cewa matukar mata suka samu ingantaccen Ilimin Addinin Musulunci a cikin al’ummar Musulmi shakka babu Ilimin zai yadu a cikin mutane sakamakon koda yaushe iyaye mata sune suke tare da yara dare da rana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!