Labarai
Hukumar KAROTA ta tabbatar da mutuwar jami’in ta sakamakon take shi da mota ta yi
Hukumar KAROTA ta jihar kano ta tabbatar da rasuwar jami’in ta anan kano.
Mai magana da yawun hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ne ya tabbatar da hakan yayin da yake yiwa Freedom Radio ƙarin bayani.
Nabulusi ya ce “hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:45 daga abokan aikin marigayin da suke a titin zuwa tsohuwar jami’ar Bayero daidai hauren shanu, inda suka shaida cewa wata babbar mota ta take abokin aikin su mai suna Zahradden Aminu Isma’il Sagagi”.
“jami’an sun shaida mana cewa marigayin yayi yunƙurin tsayar da babbar motar dakon kayan ne, sakamakon gudun wuce sa’a da direban motar ke yi, sai dai ko da ya tsayar da shi sai ƙi tsayawa kuma nan ta ke ya bi ta kan sa” a cewar Kofar Na’isa.
Jam’in hulɗa da jama’ar ya ce, tuni suka yi nasarar kama direban motar tare da miƙa shi ga rundunar ƴan sanda don faɗaɗa bincike.
Hukumar ta jaddada cewa aikin ta ne binciken kowacce mota musamman idan suna zargin ta, don kiyaye shigowa da wasu abubuwan da ba su dace ba a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login