Labarai
Hukumar kashe gobara ta ja kunnen yan kasuwa kan ajiye abubuwan da ke tada wuta

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bukaci ‘yan kasuwa da su guji aje duk wani abu da zai iya haifar da tashin gobara a cikin kasuwannin su musamman a wannan lokaci da yanayin sanyi ke kara kankama.
Jami’in hukumar Jamilu Abdullahi, ne ya yi wannan gargadi yayin taron wayar da kan ‘yan kasuwar sabon gari domin gudun tashin gobara da kasuwar ta shirya hadin gwiwa da hukumar kashe gobarar.
Da ya ke jawabi shugaban kasuwar ta Sabon Gari da Singa da Galadima, Alhaji Abdul Bashir Hussain, da mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin kasuwar Sabon Gari Musbahu Abdullahi Shadow, ya wakilta ya yi bayyana irin matakan da za su dauka na ganin sun kare kasuwannin daga faruwar iftila’in gobarar.
You must be logged in to post a comment Login