Labarai
Hukumar kididdiga: an samu hau-hawan farashin kayayyaki
Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da rahoton farashin kayayyaki, wanda ke nuni da cewa an samu hau-hawar farashin kayayyaki, idan aka kwatanta da kaso 15 da digo tara na watan Nuwambar bara, da kuma kaso 15 da digo 37 a watan Disambar da ya gabata.
Sakamakon rahoton na watan Disambar da ya gabata, na nuni da cewa an samu koma bayan, idan aka kwatanta da rahoton raguwar farashin kayayyakin da take fitarwa a baya.
Rahoton ya kara da cewa an samu hau-hawar farashin kayayyaki da kaso 15.78 a biranen kasar nan, idan aka kwatanta da kaso 16.27 da ta fitar a watan Nuwamba, yayinda kuma aka samu raguwar hau-hawar farashin kayayyakin daga kaso 15.59 zuwa kaso 15.02 a watan Disambar bara a kauyuka.
A rahoton wata-wata kuma hukumar ta NBS ta bayyana cewa shima an samu hau-hawar farashin kayayyaki a birane, sai kuma kauyukan da shima aka samu raguwar hau-hawar farashin kayayyaki a watan Disamba, idan aka kwatanta da rahoton watan Nuwambarar bara da ta fitar.