Kiwon Lafiya
Hukumar kididdiga ta kasa ta ce tattacen man fetur da aka shigo da shi bara ya kai naira tiriliyan biyu
Hukumar kididddiga ta kasa (NBS), ta ce adadin tataccen man fetur da kasar nan ta shigo da shi daga ketare a shekarar da ta wuce ya kai naira tiriliyan biyu da biliyan dari biyu da tamanin da tara.
Hakan na cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta fitar game da kididdigar adadin man fetur da kasar nan ta shigo da shi jiya.
A cewar rahoton na NBS a watanni hudun farko na shekarar an shigo da tataccen mai da ya kai na sama da naira biliyan dari takwas da biyu yayin da watanni hudu na tsakiyar shekara aka shigo da man da ya kai na sama da naira biliyan dari bakwai da arba’in da hudu. Haka kuma a watanni hutun karshen shekara an shigo da man da ya kai sama da naira biliyan dari bakwai da arba’in da biyu