Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar kididdiga ta kasa ta ce tattacen man fetur da aka shigo da shi bara ya kai naira tiriliyan biyu

Published

on

Hukumar kididddiga ta kasa (NBS), ta ce adadin tataccen man fetur da kasar nan ta shigo da shi daga ketare a shekarar da ta wuce ya kai naira tiriliyan biyu da biliyan dari biyu da tamanin da tara.

Hakan na cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta fitar game da kididdigar adadin man fetur da kasar nan ta shigo da shi jiya.

A cewar rahoton na NBS  a watanni hudun farko na shekarar an shigo da tataccen mai da ya kai na sama da naira biliyan dari takwas da biyu yayin da watanni hudu na tsakiyar shekara aka shigo da man da ya kai na sama da naira biliyan dari bakwai da arba’in da hudu. Haka kuma a watanni hutun karshen shekara an shigo da man da ya kai sama da naira biliyan dari bakwai da arba’in da biyu

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!