Labaran Wasanni
Hukumar kokawar zamani ta Najeriya ta gayyaci ‘yan kokawa 32 a zagayen farko
Hukumar kokawar zamani ta Najeriya wrestlers NWF ta gayyaci ‘yan kokawar wresting guda 32 a zagayen farko don shirye-shiryen tunkarar gasar kokawar zamani ta kasashe rainon Ingila ta bana, Commonwealth.
Wakilin mu na fagen wasanni Abubakar Musa Labaran ya ruwaito cewa gasar zata gudana a Gold Coast da Queensland da kuma Australia a ranar 4 zuwa 14 ga watan Afrilun bana.
Sakataren hukumar kokawa zamani ta kasa Ahmed Abdullahi ya ce ‘yan wasan kokawa zamanin karo na farko zasu halarci sansanin horon ranar 5 zuwa 12 ga watan Janairun da muku ciki inda karo na biyu zasu shiga sansanin bayyana sun kammala daga bisani kuma sansanin na uku.
Cikin ‘yan wasan da suka halarci sansanin horon hada dan kokawa kasar nan na daya a nahiyar Afrika a jadawalin da hukumar kokawa zamani ta duniya ta fitar, cikin rukunin ajin masu nauyi kilogram 48kg Mercy Genesis.
A wani labarin kuma, dan wasan kasar nan dan asalin jihar Kano da yake taka leda a kungiyar Ostasin FK da ke kasar Sweden Alhaji Salisu Gyero, ya ce kungiyar sa ta shirya tsaf don karawa da kungiyar Arsenal ta kasar Ingila a gasar cin kofin EUROFA a zagaye 32 na gasar.
Ya kuma bayyana rashin jajircewa ga ‘yan wasan Arewacin kasar nan da suke yi a harkokin kwallon kafa wanda shine ke haifar musu da koma baya.
Wasannin sada zumuncin da suka gudana a birnin Kano da kewaye a jiya.
A gasar frimiyar kasar Ingila wasannin da suka gudana a jiya.
Southampton 1-2 Crystal Palace
Swansea City 0-2 Tottenham Hotspur
West Ham United 2-1 West Bromwich Albion
Manchester City 3-1 Watford