Kiwon Lafiya
Hukumar KSCPC ta gano jabun magunguna na fiye da Miliyan 100

Hukumar kare hakkin masu siye da masu siyar da kayayyaki ta jihar Kano watau Kano state consumer protection Council, ta gano jabun magunguna na Sama da Naira miliyan dari da aka killace su a wani Rumbun adana kaya a kasuwar sayar da magunguna ta ƴan fata da ke bayan Bata a Kano.
Shugaban hukumar Dakta Umar Garba, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa, sun samu bayanan sirri ne game da lalatattun magungunan don haka suka je domin tabbatarwa.
Salisu Datti shi ne sakataren kungiyar masu sayar da magani ta Yan fata bayan Bata, ya ce, kungiyar ce da kanta ta tattara lalatattun magungunan daga wajen mambobinta ta kuma miƙa wa hukumar.
Daga bisa hukumar ta kare hakkin masu saye da masu sayar da kayayyaki, ta ce, za ta ci gaba da bibiyar kasuwanin Kano domin magance jabun magunguna.
You must be logged in to post a comment Login