Labarai
Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali ta Kano ta umarci jami’anta su tsaurara tsaro

Hukumar kula da Gidajen Ajiya da Gyaran Hali ta Najeriya shiyyar Kano, ta umarci dukkan jami’anta da su ƙara zage damtse wajen tabbatar da tsaro a gidajen faɗin jihar.
Mai magana da yawun hukumar Musubahu Lawan Kofar Nassarawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Freedom Radio.
A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne domin kare lafiyar fursunoni, da ma al’ummar dake kewaye da gidajen yarin,’’ tare da hana duk wani yunƙurin tayar da hankali ko tserewa.
You must be logged in to post a comment Login