Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Aregbesola: A harbe duk wanda ya nemi tada zaune tsaye a gidan gyaran hali

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gidajen gyaran hali da ke fadin kasar nan baki daya a matsayin wasu wurare na musamman da aka kebe da ke da matsanancin tsaro.

 

Saboda haka ta bai wa jami’an hukumar kula da gidan gyaran hali damar bindige duk wanda aka sake ganin yana neman tada zaune tsaye a harabar su.

 

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ya ba da wannan umarni jim kadan bayan kammala wani taron gaggawa da kwamandojin hukumar kula da gidan gyaran hali da ke kasar nan.

 

Ministan ya kuma ja kunnen jami’n hukumar kula da gidan gyaran hali da su guji yin hadin baki da daurarru suna yi musu safarar kayayyaki yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani mai yi mata zagon kasa ba.

 

Wannan na zuwa ne makwanni bayan hare-haren da aka kai wasu gidajen gyaran hali da ke sassa daban-daban na kasar nan

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!