Labarai
Mun yi asarar tiriliyan 1.3 a bana- Hukumar Kwastam
Hukumar hana fasaƙwauri ta Nijeriya Kwastam, ta ce, ta yi asarar sama da Naira tiriliyan 1 da biliyan 3 a bana sakamakon rangwame da gwamnatin tsohon Shugaban Muhammadu Buhari ta yi wa masu zuba jari.
Babban Kwanturolan hukumar Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a zauren majalisar dattawa jiya Laraba.
Adeniyi wanda ya samu wakilcin mataimakin Kwanturolan hukumar Mba Musa yayin taron sauraron ra’ayin jama’a da kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar dattawa suka shirya, wanda ya yi duba kan tsarin kashe kudade na matsakaicin wa’adi na shekarar 2024 zuwa 2026 da dabarun kasafin kudi.
A yayin zaman dai, ‘yan majalisar dattawan sun tambayi hukumar kwastam kan ta yi cikakken bayani bisa yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta rattaba wa hannu domin sabunta hukumar ta kwastam.
Idan za a iya tunawa majalisar zartaswa a watan Afrilun 2023 ta amince da aikin zamanantar da hukumar kwastam, duk da umarnin kotu da ya hana gwamnatin tarayya ci gaba da wannan shiri.
Sai dai gwamnatin Buhari ta amince da aiwatar da aikin zamanantar da hukumar.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login