Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwastam – ta yi wawan kamu na fiye da miliyan 70

Published

on

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa kwastam mai kula da shiyyar Kano da Jigawa ta kama kayayyakin da aka yi fasa kwaurin su da kudin su ya tasamma fiye da Naira milyan saba’in da tara.

Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da kwanturolan hukumar Nasiru Ahmad ya gudanar a shalkwatar hukumar anan Kano.

A cewar sa, hukumar ta kama kayan yayin rangadin da ta gudanar, inda ta kama shinkafa ‘yar waje da takin zamani da kuma tabar wiwi da kuma mutanen dake da alaka da kayan.

Nasiru Ahmad ya kara da cewa bata garin na amfani da yankin garin Babura don shigo da kayayyakin da ake fasa kwaurin su.

Ya kuma bukaci shugabannin bangaren da suyi dukkan mai yiwuwa don ganin an kawo karshen wannan matsala, da kuma tallafawa hukumar wajen kawo karshen ayyukan bata gari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!