Labarai
Hukumar Kwastom ta ce za ta hada kai da yan kasuwa wajen magance bata gari

Hukumar hana fasakwauri ta kasa Kwastom ta ce za ta hada kai da yan kasuwa wajen magance bata garin dake shigo da gurbatattun kaya kasar nan.
Shugaban hukumar mai lura da jihohin Kano da Jigawa, Abubakar Dalhatu ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai cibiyar kasuwanci ta jihar Kano dan kara kulla alakar aiki da yan kasuwa.
A cewar sa dole sai hukumar ta hada kai da yankasuwa musamman manyansu za ta iya magance bata garin da hukumar ke kamawa.
Da ya ke jawabi shugaban cibiyar kasuwancin ta jihar Kano Ambassador Usman Hassan Darma, ya ce za su bawa hukumar ta Kwastom dukkan gudunmawar data kamata wajen aikin su.
You must be logged in to post a comment Login