Connect with us

Manyan Labarai

Hukumar NAFDAC ta dakatar da kamfanin pure water 17 a jihar Kaduna

Published

on

Hukumar da ke kula da magunguna da ingancin abinci wato NAFDAC ta tsayar da wasu kamfanonin sarrafa ruwan leda goma sha bakwai aiki a jihar Kaduna sakamakon wasu laifuka da suka aikata.

Shugaban hukumar Mr Natim Mullah-Dadi ne ya bayyana haka a lokacin da suka kai ziyarar gani da ido wadannan kamfaninka a yunkurinsu na tabatar da an bi doka an sarrafa wannan ruwa cikin tsafta da tsari.

Ya bayyana cewa wadannan kamfanoni na gudanar da ayyukansu ne ba bisa ka’ida ba, wasu daga cikinsu kuma suka canza wuraren da suke sarrfa ruwan ba tare da izinin hukumar NAFDAC ba, yayin da wasu lasisi da wa’adin da ake ajeye wa ruwan ya wuce.

Ya kara da cewa duk kamfanin da suka rufe sakamakon makamancin wannan laifi ne, kuma ana dakatar da su ne har sai sun bi doka.

Mullah-Dadi ya ce hukumar ta shiga cikin damuwa sakamakon rashin kyauwun indan ake sarrafa wannnan ruwa , inda ya ce sun kwace wasu kayan aiki da injinan da suke amfani da su a kamfanin har sai kun bi ka’idojin da aka gindaya musu.

Ya kuma ja hankalin masu harkar pure water da su kauracewa amfani da wuri mara tsafta sannan su tabbatar suna gudanar da aikinsu ne bisa ka’idoji da izinin da aka basu.

Sun kuma ja hankalin jama’a da su tabbata sun lura da lamba NAFDAC kafin su sayi ruwan da zasu sha

Coronavirus

Masu Corona 759 ke jinya a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da kamuwar mutane 3 da cutar Covid-19 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter da misalin 11:29 na daren Alhamis.

Har ila yau, karin mutane 4 sun warke daga cutar kuma tuni aka sallame su a ranar Alhamis din.

Yazuwa yanzu mutane 939 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Corona a jihar Kano, 139 daga ciki sun warke, sai mutane 41 da suka rigamu gidan gaskiya.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta ce yanzu haka masu dauke da cutar 759 ke cigaba da samun kulawar jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu cutar dake nan Kano.

Continue Reading

Coronavirus

An samu raguwar masu cutar Corona a ranar Alhamis

Published

on

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta sanar da samun sabbin masu dauke da cutar COVID-19, 182 a jihohi 15 na kasarnan da birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta wallafa hakan ne a daren Alhamis ta shafinta na Twitter.

NCD ta kamar kullum jihar Legas ce ke kan gaba wajan adadin mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar da mutane -111babban burinin tarayya Abuja ta samu mutane -16 jihar Akwa Ibom mutane-10, jihar Oyo mutane-8.

Jihohin Kaduna da Delta na da mutane 6-6 yayin da jihar Rivers keda mutane-5, jihohin Ogun da Ebonyi mutane 4-4 suka kamu jihar mutane Kano-3 jihohin Plateau da  Gombe da kuma Kwara mutane 2-2 suma jihohin Kebbi da   Bauchi da  Borno mutum 1-1.

Mutane 8,915 suka kamu da cutar a sassan kasar nan daban daban.

Daga ciki mutane 2,592 sai kuma mutane 259 da cutar ta hallaka.

Adadin mutum 182 da aka samu a ranar Alhamis shine adadi mafi karanci cikin kwanaki 12 da suka wuce inda a kullum ake samun masu dauke da cutar sama da 200 a kasar.

Continue Reading

Labarai

Tambuwal zai gana da Buhari kan harin ‘yan ta’adda a Sokoto

Published

on

Fadar shugaban kasa ta shirya ganawa tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da gwaman jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kan kazamin harin da aka kai a daren ranar Laraba wanda ya shafi wadanda ba su ji ba ba su gani ba, a yankin kudu maso gabashin jihar ta Sokoto.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyan hakan ta cikin wata sanarwar da mai baiwa gwamnan shawara kan kafafan yada labarai Muhammad Bello ya sanya wa hannu.

Sanarwar tace gwamnan ya jajantawa al’ummar da harin ya shafa sannan gwaman ya baiwa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA umarnin ta ziyarci wurin da aka kai harin domin tan-tance irin barnar da aka aikata da kumar samar da kayan jin kai ga mutanen da harin ya shafa.

Tambuwal ya shaidawa masu rike da masarautun gargajiya da masu ruwa da tsaki na yankin cewa bayan tattaunawa tsakanin jiya da yau da fadar shugaban kasa ya samu gayyata domin ganawa da shugaban kasa domin shawo kan alamarin.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,753 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!