Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shirin “Kwana Casa’in” ya sanya nayi suna –Malam Ali

Published

on

Jarumin wasan kwaikwayon nan Abdul’aziz Shua’ibu wanda aka fi sani da Malam Ali ya ce masana’antar Kannywood ya fara shiga kafin fitowar sa a wasan kwaikwayon nan mai nisan zango na Kwana Casa’in.

A yayin wata tattaunawa da yayi da Freedom Radio jarumin ya ce shirin Kwana Casa’in shi ne ya fito da shi bayan da ya kwashe fiye da shekaru biyu a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Ya kara da cewa shirin Kwana Casa’in Duniya ce saboda kayayyakin da ake amfani da shi sun wuce sa’a da sauraran yadda ake shirya fina-finan hausa.

Abdul’aziz Shu’ibu yace masu shirya fim din Kwana Casa’in suna da kwarewa da gogewa wajen tsara shirin fim, kuma shi ne ya kara karfafa masa gwiwa saboda yadda ake tattalin jarumai.

A karshe jarumin ya godewa masoyan sa saboda nuna masa soyayya da suke.

 

Jarumi Abdul’aziz Shu’aibu dai na daya daga cikin manyan jaruman da tauraruwar su ke haskawa a fitaccen wasan kwaikwayon nan mai nisan zango na tashar Arewa 24 wato “Kwana Casa’in”.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!