Kiwon Lafiya
Hukumar NCC ta musanta cewar mazauna kusa da karfunan sadarwa ka iya kamuwa da cutuka
Hukumar sadawar ta kasa shiyyar Kano wato NCC, ta musanta cewa jama’a da ke makwabtaka da wuraren da aka girke karfunsn sadawar wanda kamfanonin sadarwa ke sakawa za su iya kamuwa da cutar daji
Babban jami’in hukumar Adamu Dawuni Amshi ne ya bayyana hakan a yau jim kadan bayan kammala shirin barka da Hantsi na nan gidan Rediyo freedom.
Ya ce, a cikin shekaru alif dari tara da casa’in kafin zuwan wayar salula na wannan zamani mutane kalilan ke cin gajiyar wayar salula, yana mai cewar a yanzu akwai kimanin mutane miliyan 140 wadanda ke amfanin da wayoyin salula a kasar nan.
Adamu Dawuni Amshi ya kuma ce a yanzu an samu ci gaba ta bangarori da dama, inda mai layi da ke neman komawa wani layin na daban ba dole ne sai ya sauya layi ba, abinda zaiyi kawai shine ya je ofishin Kamfanin sadarwar da yake son ya koma amfani da layinsu za su iya sauya masa kuma ya ci gaba da amfani da layin nasa.
Ya kara da cewa hukumar ta kasa kasar nan zuwa kashi 7 domin samun saukin gudanar da ayyukanta.