Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar NDLEA ta kama mashahurin dan kasuwa a filin jirgi dauke da Cocaine

Published

on

Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ce ta cafke wani babban ɗan kasuwa dauke da hodar Ibilis mai nauyin Kilo Giram 1 da kuma Tabar Wiwi.

Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter.

A cewar hukumar, jami’anta sun cafke dan kasuwar Mista Molokwu Nwachukwu, a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

NDLEA, ta ce ta cafke shi ne a kan hanyarsa ta zuwa kasahen Vietnam da Brazil da Italiya a ranar 22 ga wannan watan da muke ciki na Maris.

Haka kuma hukumar ta ce, ɗan kasuwar mutum ne da ke yawan ziyartar kasashen China da Dubai da Pakistan da Vietnam.

Hukumar ta kara da cewa ta aame shi da dauri Talatin da shida na Hodar Ibilis a cikin jakankun da kuma takalmansa lokacin da yake shirin hawa jirgi zuwa ƙasashen da ke kudancin Asiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!