Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar NECO ta sanya ranar ci gaba da rubuta jarrabawar

Published

on

Humumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta NECO ta ce za a ci gaba da rubuta jarrabawar a ranar litinin mai zuwa 9 ga watan nuwamban da muke ciki.

Hakan na cikin sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Azeez Sani ya sanyawa hannu aka raba ga manema labarai.

Idan za a iya tunawa hukumar shirya jarrabawar ta NECO ta dage ci gaba da rubuta jarrabawar sakamakon zanga-zangar Endsars da ta rikide zuwa ta’addanci a wasu jihohin kasar.

Sai dai hukumar na sanar da cewa za a ci gaba da rubuta jarrabawar a ranar litinin din mako mai kamawa kuma za a kammala a ranar 28 ga watan na nuwamba.

Sanarwar ta bukaci dalibai su nemi sabuwar jadawalin rubuta jarrabawar da za a sake ta a ranar 4 ga watan da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!