Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashawa : An sake gurfanar da shugaban hukumar tattara haraji a karo na biyu

Published

on

A Karo na biyu cikin kwanaki biyu tsohon shugaban hukumar tattara haraji ta kasa Babatunde Fowler ya sake gurfana gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC don amsa tambayoyi.

A jiya Litinin ne hukumar ta EFCC ta gayyaci Babatunde Fowler da ya gurfana gabanta don amsa tambayoyi kan zarginsa da hannu a wata almundahana.

Rahotanni sun ce a jiya Litinin din hukumar ta EFCC ta kwashe tsawon awanni bakwai ta na yiwa tsohon shugaban hukumar ta FIRS tambayoyi kan zargin wani kamfani da kaucewa biyan haraji da ya kai naira biliyan dari.

Da ya ke zantawa da manema labarai a yau, mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwajaren, ya ce tsohon shugaban hukumar tattara haraji ta kasar yana da tambayoyi da dama da ya kamata ya ba da amsarsu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!