Labarai
Hukumar NiDCON ta karbi mutane 13 da aka yi safararsu zuwa Ghana da Mali

Hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen ketare NiDCON, ta karbi wasu mutane 13 da aka yi safararsu zuwa kasashen Ghana da Mali.
Shugabar hukumar Abike Dabiri-Erewa, ce ta tarbi wadanda aka dawo da su din da suka hada da ‘yan mata 12 da karamin yaro 1 dan shekara biyar.
Ta cikin sanarwar da hukumar ta fitar ta ce, daga cikin ‘yan matan da aka ceto din sun bayyana cewa an yaudare su ne tare da tilasta musu shiga munanan ayyuka bayan an ce za a sama musu aiki a Ghana da Mali.
Haka kuma, yan matan sun kara da cewa, waɗanda suka yi safarar su din suna cin zarafin su.
You must be logged in to post a comment Login