Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NAPTIP ta ceto yara mata 11 da akayi yunkurin safararsu zuwa Libya

Published

on

Hukumar yaƙi da fataucin bil-Adama ta Najeriya NAPTIP ta ce, ta ceto wasu yan mata 11 da aka yi yunkurin safararsu daga kasarta zuwa kasar Libya.

A cewar NAPTIP an gudanar da bincike kan yunkurin safarar ‘yan matan daga Jamhuriyar Nijar lokacin da wata ƙungiyar masu safarar mutane ke niyyar jigilar su zuwa ƙasar Libya.

Kwamandan hukumar NAPTIP shiyyar Sokoto, Abubakar Tabrane  ya shaida hakan ga manema labarai, yana mai cewa jami’an hukumar kula da shige da fice ta ƙasa ne suka karɓi ‘yan matan.

Sai dai ya ce, tuni suka fara bincike da nufin kamo waɗanda ake zargi da safarar ƴan matan, wadanda tuni suna hannun hukumar NAPTIP ta Sokoto.

Rahoton:Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!