Labarai
Hukumar NiMet ta fitar da sabon hasashen yanayin da za a fuskanta

Hukumar kula da harkokin yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama hade da tsawa a sassa daban-daban na kasar daga yau Talata zuwa Alhamis mai zuwa.
Hasashen wanda hukumar ta fitar a baya bayan nan a birnin tarayya Abuja, ya ce akwai yiwuwar cewa za a fuskanci hadari hade da walkiya da tsawa a jihohin Katsina da Kano a yau Talata.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar samun hadari da tsawa mai karfi a jihohin Taraba da Adamawa da kuma zafin rana, yayin da yankin Arewa ta Tsakiya, ake sa ran sararin samaniya za ta kasance da hadari kadan tare da walkiya da tsawa a Nasarawa da Kogi da Kwara, sai Benue da kuma birnin tarayya Abuja.
Hukumar ta Nimet , ta kara da cewa a yankin Kudu kuwa, hasashen ya nuna za a samu saukar ruwa, sannan tsawa ta biyo baya a jihohin Akwa Ibom da Cross River, sai Rivers da kuma Bayelsa.
You must be logged in to post a comment Login