Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kimiyya

Hukumar kula da yanayi ta kasa NIMET ta yi hasashen samun rana mai zafi tsawon kwanaki 3 a kasar nan

Published

on

Hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi hasashen cewa za’a samu rana mai zafi  tsawon kwanaki 3 daga Litinin din nan zuwa Laraba a fadin kasar nan.

Rahoton hasashen da hukumar ta fitar ranar Lahadi ya nuna cewa akwai yiwuwar samun tsawa mai karfi a sassan jihohin Yobe da Adamawa da Gombe sai Kaduna da Taraba.

A cewar hasashen, ana sa ran samun ruwan sama tsawon kwanaki 3 a jihohin Ogun da Ondo da Osun da Imo da Edo da Enugu da Anambra da Ekiti da Lagos da Rivers da Akwa Ibom sai Bayelsa da Delta da kuma Cross River.

Haka kuma hukumar ta yi hasashen yankin arewa ta tsakiya zai kasance cikin hadari da tsawa a sassan Nasarawa da Filato da Benue da Neja sai Kogi da Birnin Tarayya a safiyar ranar talata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!