Connect with us

Labarai

Hukumar NiMet ta fitar da sabon rahoton hasashen yanayi

Published

on

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen samun hazo a wasu jihohin Arewacin Najeriya daga  yau Litinin zuwa Laraba.

Hakan na kunshe a  cikin sanarwar da Hukumar NiMet ta fitar a Daren jiya Lahadi.

Sanarwar ta nuna cewa a ranar Litinin ana sa ran hazo a sassan Jihohin Kebbi da Kano, inda nisan gani zai ragu zuwa tsakanin kilomita biyu zuwa biyar, yayin da sauran jihohin Arewa su ma za su fuskanci hazo.

A ranar Talata kuma ana sa ran hazo mai sauki a wasu sassan Kano da Kebbi, yayin da sauran jihohin Arewa za su ci gaba da kasancewa cikin hazo mai ƙura.

Hukumar ta ce a ranar Laraba dukkan jihohin Arewa za su ci gaba da kasancewa cikin hazo mai ƙura, tare da shawartar al’umma musamman masu matsalar numfashi su dauki matakan kariya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!