Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a samu hazo a wasu jihohin Nijeriya- NIMET

Published

on

Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasa NIMET, ta ce za’a fuskanci hazo mai cike da kura da kuma kwallewar hasken rana daga yau Asabar zuwa Jibi Litinin.

Wannna na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, cewar yanayin zai fara tun daga safiyar yau Asabar ne zuwa yammacin jibi Litinin a wasu sassan kasarnan.

Ta cikin Sanawar hukumar ta ce, yanayin hazon zai mamaye jihohin da ke Arewa ta tsakiya da kuma wasu jihohin a kudancin kasar nan da suka hadar da Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom da kuma Cross River.

Sanarwa ta shawarci al’umma da su kare kansu daga shakar kurar, kasancewar zata iya zama babbar illar ga lafiya.

 

Labaran:Aisha Muhammad Yarleman

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!