Kiwon Lafiya
Hukumar NIMET ta yi hasashen samun ruwan saman a safiyar Alhamis mai zuwa a wasu jihohin Najeriya
Hukumar dake kula da yanayi ta Najeriya NIMET ta yi hasashen yanayin samun ruwan sama da za’a yi da safiyar jibi Alhamis a jihohin Gombe da Kaduna da Bida a jihar Neja.
Hasashen wanda babban jami’in da ke kula da yanayin jihohin ta Tsakiya a Abuja ya kuma yi hasashen yadda yanayin jihohin za su shiga kan ma’aunin Celsius 25 da 34 da 16 da kuma 24.
Haka zalika hukumar ta NIMET ta ce ana kyautata zaton za’a samu ruwan sama ba-kakautawa a daukacin yankin da rana da kuma yammaci a jihohin
A yayin da hukumar ta sake yin hasashen samun ruwan sama a wasu daga cikin jihohin kudancin kasar nan da safiya da rana da kuma yammacin ranar Alhamis din Kasancewar yanayin zai kama ne daga 29 da 30 da 21 da 23 a ma’aunin Celsius.
A cewar, hukumar ta NIMET jihohin arewacin kasar nan da safiyar ranar Alhamis za su fuskanci ruwan sama mai karfi tare da tsawa da cida da suka hada da Katsina da Kano da Dutse a jihar Jigawa da Nguru a jihar Yobe da Zaria a jihar kaduna da kuma garin Potiskum.
A saboda hakan ne kumar ta bukaci al’umma da su kwan da shirin ko-ta-kwana don kare kan su daga ambaliyar ruwan sama a yankunan su.