Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kakaba wa Sudan ta Kudu takunkumin haramta mata sayen makamai

Published

on

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, ya kakabawa kasar Sudan ta Kudu takunkumin haramta mata sayen makamai.

Kudurin da Amurka ta gabatar dai ya samu amincewar kwamitin ne bayan samun kuri’u 9 da ya ke bukata a zauren kwamitin tsaron, yayin da Rasha, China, Ethiopia, Bolivia, Equatorial Guinea da Kazakhstan suka ki amincewa da kudurin, bisa dalilan cewa bangaren gwamnati da na ‘yan tawayen kasar kan kokarin cimma tabbataccen sulhun kawo karshen yakin kasar.

Amurka da wasu kasashen Turai sun jima suna kiran da a kakabawa Sudan ta kudu takunkumin cinikin makamai, sai dai Amurka ta gaza samun nasara kan bukatar a watan Disambar shekarar 2016, da ta mika kudurin ga kwamitin tsaron na Majalisar dinkin duniyar.

A shekarar 2013, yakin basasa ya barke a Sudan ta Kudu shekaru 2 bayan samun ‘yancin kai daga Sudan.

Rikicin ya fara ne bayan da shugaban Sudan ta Kudun Salva Kiir ya zargi mataimakinsa Riek Machar da yunkurin yi masa juyin mulki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!