Labarai
Hukumar NPA ta baiwa hukumar SON da NAFDAC wa’adin awa 24 da kwashe nasu ya nasa a tashoshinta
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa ta baiwa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC da kuma hukumar kula da inganci kayayyaki SON wa’adin awanni ashirin da hudu da su kwashe nasu ya nasu su bar tashoshin jiragen ruwan kasar nan.
A cewar hukumar ta NPA duk jami’in hukumomin biyu da aka samu a tashoshin jiragen ruwan kasar nan bayan cikar wa’adin awanni ashirin da hudu za a kama shi a kuma gurfanar da shi gaban kuliya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da babban manaja mai kula harkokin yada labarai na hukumar Abdullahi Goje ya fitar jiya a Lagos.
Sanarwar ta ce daukar matakin ya zama wajibi domin yin biyayya ga umurnin da kwamitin koli da shugaban kasa ya kafa don saukaka gudanar da kasuwanci a kasar nan ya bayar a kwanakin baya.
Ta cikin sanarwar dai an kuma ruwaito shugaban hukumar Hadiza Bala Usman na cewa hukumomin gwamnati takwas ne kawai aka amince da su gudanar da ayyuka a tashoshin jiragen ruwan.
Hadiza Bala Usman ta cikin sanarwar dai ta ce; hukumomin da aka amince su yi aiki a tashoshin jiragen ruwan sun hada da: hukumar ta NPA da hukumar yaki da fasakwauri ta kasa da hukumar kula da tsaron gabar ruwar kasar nan NIMASA da rundunar ‘yan-sandan kasar nan da kuma hukumar tsaron sirri ta DSS.
Sauran sun sune: hukumar kula da shige da fice ta kasa da jami’an lafiya da kuma hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.