Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar NYSC ta kara wa masu yi wa kasa 3 wa’adi saboda aikata laifi

Published

on

Hukumar kula da hidimar kasa wato NYSC ta kara wasu masu yi wa kasa hidima wa’adi sakamakon wasu laifuka da wasu masu yi wa kasa hidima su uku suka aikata a jihar Gombe.

 

Mai kula da shirin na yi wa kasa hidima a jihar Gombe Mr David Pwanidi Markson ne ya bayyana haka a yau a yayin bikin yaye masu yi wa kasa hidima rukuni “C” a jihar ta Gombe.

 

Ya ce daga cikin masu yi wa kasa hidima 1,153 wadanda suka kammala yiwa kasa hidima, guda takwas daga cikinsi sun samu lambar girmamawa, yayin da wasu hudu suka karbi takardar yabo sai kuma wasu uku da suka samu karin wa’adi na yiwa kasa hidima kafin a yayesu.

 

Mr Markson ya kara da cewa daga cikin masu yi wa kasa hidima wacce ta lashe mafi kwazo, mace ce mai suna Olabajo Damilola Racheal mai lamba GM/18C/1377

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!