Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Adamawa

Published

on

Rundanar yan sanda ta kama wasu masu garkuwa da mutane su biyu a karamar hukumar Song dake jihar Adamawa.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yansanda ta jihar DSP Sulaiman Yahaya ne ya tabbatar da faruwar hakan a Yola.

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewar an kama masu garkuwan ne bayan sun rubuta wata wasika na razani ga iyalan wani da suka yi garkuwa da shi, inda suka tsorotar da su akan wasu adadin kudaden da suka bukata.

DSP Sulaiman ya ce tuni aka fara binciken kuma za’a gurfanar da masu laifin gaban kotu, sannan ya tabbatar da ceto farfesa Adamu Zata wani malami a jami’ar kimiyya ta Modibbo Adama dake Yola, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar litinin din da ya gabata.

Suleiman Yahaya dai bai bayyana yadda aka ceto farfesa Adamun ba, an dai sako shi ne a jiya da misalin karfe 9 zuwa 10 na yammancin jiya.

An sace farfesa Adamu ne a safiyar litinin, inda suka harbi kanin farfesa Dr. Sheda Zata likitan dabbobi, a lokacin da yayi kokarin shiga tsakani wanda tuni dai ya rasa ransa.

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka yi garkuwa da farfesa Adamun.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!