Labarai
Hukumar PCACC ta kwato tare da mayar da kusan Naira Miliyan 40 ga masu korafi

Hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC, ta mayar da kudade wadanda ta kwato daga hannun mutanen da aka yi korafi a kansu tare da mayar da kudin ga masu su.
Shugaban hukumar Sai’du Yahaya, ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a ganawarsa da manema labarai, yayin da hukumar ke shirin mayar da kusan Naira Miliyan 40 ga masu su.
Haka kuma, Shugaban hukumar ta karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC, ya kara da cewa, wannan ne karon farko da hukumar ta fara bayar da cakin kudi ga mutanen da ta bibiyi hakkokinsu tare da karbo kudaden da aka danne musu.
” A baya mun saba tura wa mutane kudadensu ne ta lambar asusun da suka cike a jikin Fom din da muke basu ta yadda ba ma sai sun kara dawowa hukumar nan ba domin karbar kudinsu, amma yanzu mun fara bayar da cakin kudin ne domin al’umma su ga irin aikin da muke yi”
Latsa alamar Play da ke kasa domin jin muryarsa.
You must be logged in to post a comment Login