Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Hukumar SEC da hadin gwiwar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano zasu magance matsalolin ‘yan damfara

Published

on

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta sha alvwashin hada kai da hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta kasa SEC wajen yaki da masu damfarar mutane wajen karbe mu su kudade da nufin sanya jari a kamfanoninsu na kasuwanci da sauran almundahanar kudade a Jihar Kano.

Shugaban hukumar Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin jami’an hukumar ta SEC da ke kula da shiyyar Kano jiya a ofishinsa.

Wannan sanarwa da daraktan ayyuka na musamman na hukumar Usman Bello ya aikowa Freedom Radio, inda ya ce hukumar ta damu matuka bisa tarin korafe-korafen da ke gabanta na zargin damfara da aka yi wa mutane da dama musamman ma mata, wajen karbe musu kudade da nufin yin kasuwanci mai riba na zamani.

A don haka ne ma hukumar ta tashi tsaye wajen kwato musu hakkokinsu, tare da hadin gwiwar hukumar ta SEC.

A na sa jawabin jagoran tawagar ta SEC Alhaji Abdulbaki Ango, wanda shi ne ya wakilci shugaban hukumar shiyyar Kano, cewa makasudin ziyar shi ne don neman hadin gwiwar hukumar ta karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, don magance wadancan matsaloli na masu damfarar mutane ta hanyar karbar kudadensu a nan Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!