Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An samu gawar saurayi da budurwa tsirara a Kano

Published

on

Rahotonni daga unguwar Badawa dake nan Kano na cewa an tsinci gawar wani saurayi da budurwa tsirara acikin dakin girki a wani gida dake unguwar.

Wata majiya ta shaidawa Freedom Radio cewa saurayin ya jima yana al’amuran sa a gidan cikin kwanciyar hankali.
Sai dai a wannan karon an samu gawarsa da ta wata da ake zargin budurwarsa ce tsirara.

Shima mai gidan da abin ya faru, ya ce iyalan sa suna can cikin gida, kuma basu san cewa matashin ya shigo zuwa dakin girkin gidan ba.

Izuwa yanzu dai muna cigaba da tattara bayanai domin kawo, muku cikakken labarin, dama jin ta bangaren hukumomin tsaro.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!