Kasuwanci
Hukumar SON shiyyar Kano ta gudanar da bikin ranar inganci ta duniya

Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON, shiyyar Kano, ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen gudanar da Bikin ranar tabbatar da inganci da daidaito ta duniya watau World Standards Day.
Hukumar tare da kamfanoni da dama da ke sarrafa kayayyaki a nan Kano inda suka gudanar da tattaki daga ofishin shiyyar Kano na hukumar da ke Sakatariyar Gwamnatin tarayya zuwa babban ofishin hukumar ta SON da ke unguwar Hotoro.
A yayin tattauna, jami’an hukumar da rakiyar jami’an tsaro har ma da wakilan ɗaruruwan kamfanoni, sun fara tattakin ne inda bayan baro ofishin hukumar na ɗaya Watau Kano 1 suka bi ta titin Katsina zuwa Wapa da Titin Ibrahim Taiwo zuwa titin Obasanjo suka bi ta titin zuwa Zaria daga nan suka hau kan titin Maiduguri kana suka isa babban ofishin hukumar da ke unguwar Hotoro watau Kano 2.
A ganawarsa da manema labarai, Daraktan hukumar ta SON mai kula da shiyyar Kano, Mista Albert Wilberforce, ya bayyana cewa, ana gudanar da taron ne a duk fadin duniya domin tabbatar da ingancin kayyayaki.
Ya ce, ana gudanar da bikin na World Standards Day ne a duk ranar 14 ga watan Oktoban kowace shekara.
Mista Albert Wilberforce, ya ƙara da cewa, “Wasu jihohin Najeriya da dama sun gudanar da nasu bikin, amma mu a nan Kano da muka nemi shawarar masu ruwa da tsaki da kuma wakilan kamfanoni kan gudanar da namu taron sai suka buƙaci da mu bari su yi shiri don a gudanar da gagarumin biki wanda kowa zai samu gamsuwa da ƙayatarwa.
Bayan kuma komai ya kammala shi ne yau muke wannan biki kamar yadda doka ta bada dama cewa kowa zai iya zaɓar ranar da zai yi nasa duk sanda ya ga dama.”
Kun ga yadda kamfanoni da yawa suka halarta kuma ga irin gudunmawar da suka bamu wasu sun kawo Abinci wasu Ruwa wasu Lemo wasu sun kawo kayayyakin da suke sarrafawa wasu sun kawo motoci, don haka muna gode musu sosai.”
Muna kuma yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, bisa yadda ya ke son kawo gyara da ci gaba a Najeriya, haka ma gwamnatin Kano musamman gwamna Abba Kabir Yusuf, muna gode masa saboda ya na bamu gudunmawa sosai.”
“Haka kuma muna amfani da wannan rana wajen bai wa wasu kamfanoni guda 15 waɗanda muka yadda da ingancin kayansu za mu basu shaidar inganci ta MANCAP a kayayyakin su guda 49, don haka yau za mu basu wannan shaida kuma muke tabbatar wa da mutane cewa lallai kayansu na da inganci su ci gaba da saya,” in ji Mista Albert Wilberforce.
You must be logged in to post a comment Login